Za'a fara tura Kudi a Asusun Ajiya na Bankuna ga Ya'yan Jam'iyyar APC
Za'a fara tura Kudi a Asusun Ajiya na Bankuna ga Ya'yan Jam'iyyar APC

An buƙaci duk wanda har yanzu ba a haɗa masa Account Number ba, da ya hanzarta zuwa wajen wanda ya yi masa rajistar domin kammala wannan muhimmin tsari.
Wannan na da muhimmanci musamman ganin cewa, bisa ga sanarwar, ana sa ran fara tura kuɗaɗe (Alert) ga mambobin da suka yi rajista kuma aka haɗa bayanan asusun bankunansu yadda ya kamata.
SHARUƊƊAN HAƊA ACCOUNT NUMBER:
1. Sunan da ke kan asusun bankinka dole ne ya yi daidai da sunan da aka yi amfani da shi wajen rajistar APC E-Membership.
2. Asusun bankin dole ne ya kasance na bankin da ke aiki a Najeriya.
3. Lambar wayar da aka haɗa da asusun bankin dole ne ta kasance a kunne kuma tana iya karɓar saƙonnin banki (SMS Alert).
4. Wanda ya yi maka rajistar APC E-Membership shi kaɗai ne zai iya shiga Portal domin haɗa Account Number ɗinka.
Ana shawartar dukkan mambobin APC da abin ya shafa da su gaggauta tabbatar da an kammala musu wannan tsari.
Comments(0)
Sign in to join the conversation
Sign In to CommentNo comments yet. Be the first to share your thoughts!
