DAGA FADAR SHUGABAN KASA
Shugaba Tinubu ya gana da wasu Mutane,bayan dawowar sa daga Umara

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana wasu ƴan tawaga ta musamman da suka kai masa ziyara a fadarsa a jiya Alhamis, waɗanda suka haɗa da gwamnonin Plateau da Taraba, Caleb Mutfwang da Agbu Kefas, Janar T.Y. Danjuma, tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, Ministan Tsaro Janar Christopher Musa da Thomas Etuh, da sauransu.
Ziyarar na da nasaba da zaɓen 2027, inda bayanai suka ce ƴan tawagar sun jaddada goyon bayansu ga Shugaba Tinubu a zaɓen 2027 da ke tafe.
Comments(0)
Sign in to join the conversation
Sign In to CommentNo comments yet. Be the first to share your thoughts!
