APC TA HANA MINISTOCHI ZUWA TARON KAMFE DA BANA JIHOHIN SU DA DA
Sabon Salon Tsarin Kamfe na Jam'iyyar APC

APC TA HANA MINISTOCHI ZUWA TARUKAN YAƘIN NEMAN ZAƁEN DABA NA JIHAR SU BA;
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta hannun Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa (PCC), ta umarci ministoci, masu riƙe da muƙaman siyasa da sauran mambobin majalisar da su halarci tarukan yaƙin neman zaɓen da za a shirya a jihohinsu na asali kawai, gabanin zaɓen shekarar 2027.
An bayyana wannan umarni ne a cikin wata takardar sanarwa da Abdulaziz Yari, Darakta-Janar na Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta APC, ya sanya wa hannu.
A cewar takardar, manufar gudanar da tarukan ita ce tattara magoya bayan APC tare da wayar da kan masu zaɓe game da nasarorin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu a lokacin mulkinsa.
Comments(1)
Sign in to join the conversation
Sign In to CommentGreat article
