TALLAFIN MAI YA TAFI FAUFAUFAU
Duk wanda ya ce zai dawo da tallafin man fetur, ƙarya yake yi, in ji Tinubu

Duk wanda ya ce zai dawo da tallafin man fetur, ƙarya yake yi, in ji Tinubu
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta iya dawo da tallafin man fetur ba, saboda dawo da shi zai jefa makoman yaran Najeriya cikin matsala.
Ya bayyana hakan ne a wurin taron gangami na jam'iyyar APC da ya gudana a Dutse da ke jihar Jigawa, inda ya ce duk wanda ya ce za a dawo da tallafin man fetur ya yi karya don fadin haka yaudarace.
Shugaban kasa ya ce kuɗin da ake kashewa wajen tallafin man fetur za a mayar da su wajen ilimi, noma da kuma samar da abubuwan more rayuwa.
Comments(0)
Sign in to join the conversation
Sign In to CommentNo comments yet. Be the first to share your thoughts!
