SOJOJIN NIGERIA SUN GAJI
Ministan Tsaron Nigeria Christopher Musa yayi korafi

Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya bayyana cewa jami’an rundunar sojojin ƙasar sun gaji matuƙa sakamakon tsawaita lokacin da suke ɗauka suna gudanar da ayyukan tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.
Ya ce sojoji da dama suna shafe shekaru ba tare da samun damar zama tare da iyalansu ba, sakamakon ci gaba da tura su ayyukan yaƙi da matsalolin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.
Ministan ya bayyana cewa wannan yanayi na haifar da babban nauyi da matsin lamba ga rundunar sojojin ƙasar.
Ya bayyana chewa lokachi yayi da za'a ba Yansanda damar su don chi gaba da gudanar da ayyukan tsaron cikin gida. Ya kuma nuna mahimmancin inganta aiki da Rayuwar iyalan jami'an Tsaron. Ya yabawa Gwamnati akan Irin temakon da takewa Kungiyar Katan Sojoji.
Christopher musa ya nemi a kara temakon Hukumar Yan sanda don inganta aiki da sanar da tsaro.
Comments(0)
Sign in to join the conversation
Sign In to CommentNo comments yet. Be the first to share your thoughts!
