HUKUMAR SMEDAN TA BUDE SABUWAR GASA
Gasar Cin Miliyan daya da wani abu

An shirya gasar ne a matsayin wani ɓangare na taron GROW Nigerian Conference 2026, wanda ake gudanarwa a birnin Legas.
A tsarin gasar, wanda zai zo na farko zai samu kyautar naira miliyan ɗaya (₦1m), yayin da waɗanda za su zo na biyu da na uku za su samu naira dubu ɗari biyu da hamsin (₦250,000) kowannensu.
Waɗanne mutane ne za su iya shiga gasar?
Gasar a buɗe take ga masu ƙirƙirar abubuwan yaɗa labarai a shafukan sada zumunta daban-daban, waɗanda suka haɗa da Instagram, TikTok, YouTube, X da sauran kafafen sadarwa na zamani.
Hukumar ta bayyana cewa ba sai mutum ya kasance fitaccen mai tasiri a kafafen sada zumunta (Influencer) ba kafin ya shiga gasar.
Haka kuma, masu farawa, waɗanda ke tasowa a harkar da kuma ƙwararrun masu ƙirƙirar abubuwan yaɗa labarai duk suna da damar shiga.
Sharuɗɗan shiga gasar
Dole ne mahalarta gasar su halarci taron GROW Nigerian Conference da kansu a Ecobank Pan African Centre da ke Victoria Island, a birnin Legas, daga ranar 8 zuwa 10 ga Nuwamba, 2026.
Ana buƙatar mahalarta su riƙa ɗaukar hotuna, bidiyo da sauran abubuwan da suka shafi taron, tare da wallafa su a shafukansu na sada zumunta ta amfani da alamar #GROWNigerian.
Duk wani abu da aka wallafa ba tare da wannan alama ba ba zai shiga cikin ƙididdigar gasar ba.
Za a tantance waɗanda suka yi nasara ne bisa jimillar martanin da abubuwan da suka wallafa suka samu a kafafen sada zumunta a tsawon kwanakin taron.
Horon kan layi kyauta ga masu neman shiga gasar
A wani ɓangare na shirin, SMEDAN ta kuma shirya horo ta yanar gizo kyauta, wanda fitacciyar 'yar kasuwa kuma mai ƙirƙirar abubuwan yaɗa labarai, Nelly Agbogu, za ta gabatar.
An tsara gudanar da horon ne a ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026, kuma waɗanda suka yi rajista za su samu bayanan yadda za su shiga ta imel ɗinsu.
Yadda za a nemi shiga gasar
Masu sha'awar shiga gasar za su iya cike fom ɗin neman shiga ta hanyar shafin SMEDAN da aka tanada musamman domin wannan gasa.
Ana buƙatar mai nema ya bayar da waɗannan bayanai:
1. Sunayen shafukansa na sada zumunta (Social Media Handles).
2. Nau'in kafafen sada zumuntar da yake amfani da su.
3. Yawan mabiyan da yake da su a kowane shafi.
4. Bayanin gogewarsa a harkar ƙirƙirar abubuwan yaɗa labarai.
5. Tabbacin cewa zai iya halartar taron da kansa a Legas.
Neman shiga gasar kyauta ne, kuma kowane mutum yana da damar aika takardar neman shiga guda ɗaya kacal.
Ranar ƙarshe ta neman shiga gasar ita ce Lahadi, 8 ga Nuwamba, 2026, da ƙarfe 11:59 na dare.
An shawarci masu sha'awar shiga gasar da su tabbatar za su iya halartar taron da kansu kafin cike fom ɗin neman shiga.
Inda za a nemi shiga gasar
Ana iya samun fom ɗin neman shiga gasar ta hanyar wannan shafi:
https://conference.smedan.gov.ng/creators
Wannan dama ce ga matasa da sauran masu ƙirƙirar abubuwan yaɗa labarai a Najeriya, musamman masu tasowa, domin nuna basirarsu, samun ƙarin farin jini da kuma cin moriyar kyaututtukan da aka tanada.
Pen Times Magazine
Comments(0)
Sign in to join the conversation
Sign In to CommentNo comments yet. Be the first to share your thoughts!
