BIKIN ROYAL FAIR 2026 YA BAR BAYA DA QURA
Sarkin Kano Sanusi na shan Chechekuche

Bikin Nuna Kwalliya da ’Yar Sarkin Kano Ta Shirya Ya Jawo Cece-Kuce
Bikin baje kolin kayan kwalliya da sutura na mata da maza (Fashion Show), wanda Sabeerah Sanusi, ’yar Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ta shirya, ya jawo muhawara a kafafen sada zumunta.
An gudanar da bikin ne inda mata da maza suka fito cikin kayan kwalliya iri-iri, suna rangadi a gaban mahalarta taron. Mai Martaba Sarkin Kano ma ya halarci wajen taron.
Wani abin da ya fi daukar hankalin jama’a shi ne yadda wata daga cikin mahalarta bikin ta cire siket dinta (na sama) bayan kammala rangadin da ta yi.
Lamarin ya haifar da ra’ayoyi mabambanta, inda wasu suka yaba da shirin, yayin da wasu ke ganin bai dace da al’adun Hausawa da koyarwar addinin Musulunci ba.
Comments(0)
Sign in to join the conversation
Sign In to CommentNo comments yet. Be the first to share your thoughts!
