A JIHAR KATSINA HUKUMAR HISBAH TA HANA TALLAR DARE
Daga Jihar Katsina

Hisbah a Katsina ta haramta wa ’yan mata talla da daddare
Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta haramta wa ’yan mata sana’ar talla da daddare a faɗin jihar, inda ta bayar da umarnin cewa dole ne su daina talla kafin ƙarfe 10:00 na dare a kowace rana.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa Kwamandan hukumar Hisbah ta jihar, Sheikh Saifullahi Yakubu Musa, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar.
Comments(0)
Sign in to join the conversation
Sign In to CommentNo comments yet. Be the first to share your thoughts!
