WANENE ALH. GARBA SALMANU YANTUMAKI?
TARIHIN MARIGANYI HON. ALH. GARBA SALMAU YANTUMAKI (1946–2016)

TARIHIN MARIGANYI HON. ALH. GARBA SALMAU YANTUMAKI (1946–2016)
Haihuwa da Farkon Rayuwa:
Hon. Alh. Garba Salmau Yantumaki an haife shi a shekara ta 1946 a Yantumaki, karamar hukumar Danmusa, wadda a wancan lokacin tana karkashin tsohuwar Safana LGA a Jihar Katsina.
Karatu:
Ya fara karatunsa a Makarantar Firamare ta Bakori (1954–1957) sannan ya ci gaba a Makarantar Firamare ta Malumfashi (1958–1960). Daga nan ya tafi Kwalejin Malamai ta Katsina (1961–1965), inda ya samu Takardar Shaidar Malanta ta Grade II a shekarar 1966. Ya kuma halarci Kwalejin Malamai ta Gaba, Sokoto (1972–1975), da Jami’ar Bayero, Kano (1977–1980), inda ya kammala digiri na farko a fanni Tarihi (B.A. History).
Shaidun Karatu:
Takardar Shaidar Malanta ta Grade II,daga Kwalejin Malamai ta Katsina, 1966
Shaidar Karatu ta UK Assisted Course, 1965
Takardar NCE, daga Kwalejin Malamai ta Gaba, Sokoto, 1975
Digiri na Farko (B.A. History), daga Jami’ar Bayero, Kano, 1980
Gogewa a Aiki:
Malami Grade II: Makarantar Firamare ta Batsari (1966)
Shugaban Makaranta: Makarantar Firamare ta Batsari (1967–1972)
Malami Grade III: na WTC Zankwa (1975)
Malami Grade II: na WTC Zaria (1976–1977)
Babban Malami: Kwalejin Malamai ta Dutsin-Ma (1980)
Mataimakin Shugaban Kwalejin Malamai: Kwalejin Malamai ta Dutsin-Ma (1981)
Sole Administrator: Tsohuwar Karamar Hukumar Dutsin-Ma (1982–1984)
Babban Jami’in Dubawa: Dutsin-Ma Zone (1984–1985)
Mukaddashin Babban Jami’in Dubawa: Dutsin-Ma Zone (1985–1988)
Daraktan Ilimin Firamare: Ma’aikatar Ilimi (1988–1989)
Daraktan Ilimi Janar: Hukumar Gudanar da Makarantun Firamare, Katsina (1989)
Sakataran Ilimi: Safana LGEA (1989–1997)
Sakataran Ilimi: Danmusa LGEA (1989–1997)
Siyasa:
Hon. Garba Salmau Yantumaki ya kasance mamba na jam’iyyar PDP. An zabe shi Shugaban Karamar Hukumar Danmusa, inda ya yi shugabanci tsawon shekara goma. Daga bisani, ya yi wa’adi a matsayin mamba a Majalisar Dokokin Jihar Katsina (2011–2015).
Legacy daya bari a Matsayin Shugaban Karamar Hukumar Danmusa:
1. Gina ginin ofisoshin sakatariyar karamar hukumar Danmusa.
2. Gina kasuwanni na zamani a Danmusa da Yantumaki.
3. Gina gidaje 30 a garuruwan Yantumaki da Danmusa.
4. Kafa Makarantar Firamare ta Bagudu a Yantumaki.
Iyali:
Ya bar yara 11: Nana Hadiza, Babangida, Hafsat, Ibrahim, Hamida, Amina, Zainab, Bello, Fufa’i, da Aliyu.
Gudummawar daya bada:
Rayuwar Hon. Garba Salmau Yantumaki ta kasance cike da sadaukarwa ga al’umma ta hanyar kokarinsa wajen bunkasa ilimi, shugabanci, da inganta ababen more rayuwa.
A matsayinsa na shugaban karamar hukuma, ya gabatar da ayyuka masu tarin yawa wadanda suka kawo ci gaba ga yankinsa. Ya kuma samu lambar yabo ta kasa saboda ayyukansa na kishin kasa da mutane.
Gadon Hon. Alh. Garba Salmau Yantumaki zai ci gaba da haskawa a matsayin abin koyi ga shugabanni da ma sauran al’umma. Ayyukansa a fannonin ilimi, shugabanci, da ci gaban al’umma sun bar tarihi mai dorewa a Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.
Salihu Ibrahim Pen times magazine
Salihu Ibrahim
Salihu Ibrahim is a Nigerian media professional, digital journalist, strategic communication practitioner, educationist and community development advocate from Yantumaki, Danmusa Local Government Area, Katsina State. He is the Chief Executive Officer (CEO) of Pen Times Media General Services and Chief editor of Pen Times Magazine, where he provides leadership, digital publishing, editorial coordination, publicity, advertising and strategic communication.
Comments(0)
Sign in to join the conversation
Sign In to CommentNo comments yet. Be the first to share your thoughts!
