SABUWAR DAMA GA MONOMA
Sabon shirin tallafawa Manoma

Gwamnatin Tarayya Ta Ware ₦200bn Domin Tallafa Wa Manoma 400,000 A Najeriya
Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta hannun Bankin Noma (Bank of Agriculture – BOA), ta ware kimanin Naira biliyan 200 domin tallafa wa manoma 400,000 a faɗin ƙasar nan a ƙarƙashin sabon shirin noman rani na shekarar 2026/2027.
Shirin, wanda ake aiwatarwa tare da haɗin gwiwar kamfanin Flour Mills of Nigeria (FMN), na da manufar bunƙasa noman alkama a cikin gida, ƙara samar da abinci da kuma rage dogaro da alkamar da ake shigowa da ita daga ƙasashen waje.
An bayyana hakan ne yayin bikin ƙaddamar da shirin noman alkama na lokacin rani a ƙauyen Maje, da ke ƙaramar hukumar Taura a jihar Jigawa.
Manajan Daraktan Bankin Noma, Ayo Sotinrin, ya ce shirin zai samar wa manoma da damar samun kuɗaɗen noma, ingantattun iri, takin zamani, magungunan kashe ciyawa da kwari, da kuma sauran muhimman kayan aikin noma.
A nasa jawabin, Manajan Yankin Arewa maso Yamma na bankin, Abdul-Razaq Datti Saleh, wanda ya wakilci shugaban bankin, ya bayyana cewa za a yi amfani da kamfanonin haɗa manoma (Farmer Aggregation Companies) wajen tantance waɗanda suka cancanci cin gajiyar shirin da kuma raba musu kayan aikin noma.
Ya ƙara da cewa adadin tallafin da kowace jiha za ta samu zai danganta da yawan manoman da abokan haɗin gwiwar shirin suka gabatar.
Yadda Manoma Za Su Amfana
Babban Manajan kamfanin Golden Agro Input Limited, wani reshe na FMN Agro, Tayo Ilori, ya bayyana cewa kamfaninsu na tallafa wa manoma 10,000 a cikin jihohi shida ta hanyar samar musu da ingantattun iri, takin zamani da magungunan noma.
Ya bayyana cewa manomin da zai noma hekta ɗaya zai samu kayan aiki da suka haɗa da:
Kilogiram 100 na irin alkama.
Buhunan takin Urea guda shida.
Buhunan takin NPK 20:10:5 guda huɗu.
Magungunan kashe ciyawa da kwari.
An kiyasta darajar waɗannan kayan aikin tsakanin Naira 250,000 zuwa Naira 350,000 ga kowace hekta.
Sai dai, kayan aikin ba kyauta ake bayarwa ba. Ana bayar da su ne bisa tsarin bashi, inda manoma za su biya bashin ta hanyar miƙa wani kaso na alkamar da suka girbe, bisa farashin kasuwa a lokacin.
Baya ga haka, za a samar wa manoma da ƙwararrun ma'aikatan gona domin ba su shawarwari kan hanyoyin shuka, amfani da takin zamani da inganta amfanin gona.
Yawan Amfanin Gona Ya Ƙaru
Manajan Shirin Bunƙasa Noman Alkama na Ƙasa a kamfanin FMN, Aliyu Ismaila, ya bayyana cewa haɗin gwiwar da ake yi wajen bunƙasa noman alkama ya fara haifar da sakamako mai kyau.
A cewarsa, matsakaicin yawan alkamar da manoma ke samu daga hekta ɗaya ya ƙaru daga tan 1.2 a shekarar 2021 zuwa tan 4.1 a shekarar da ta gabata.
Shirin na wannan kakar kuma yana da burin taimaka wa wasu manoma su iya samun tan biyar zuwa bakwai na alkama daga hekta ɗaya.
Yadda Za A Samu Tallafin
Manoman da ke sha'awar cin gajiyar shirin ana buƙatar su kasance cikin ƙungiyoyin manoma ko haɗin gwiwar kamfanonin da Bankin Noma ya amince da su.
Haka kuma, bayanai kan tantance manoma sun nuna cewa ana iya la'akari da girman gonar da suke nomawa, katin shaidar zama ɗan ƙasa (NIN), lambar tantance asusun banki (BVN) da tarihin ayyukan noman da suke gudanarwa.
Manoma za su iya tuntuɓar ƙungiyoyin manoma da aka amince da su, musamman All Farmers Association of Nigeria (AFAN), ko kamfanonin haɗa manoma domin samun ƙarin bayani kan yadda za su shiga shirin.
Ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a sanar da wani cikakken shafin yanar gizo na neman tallafin kai tsaye ko wa'adin rufe neman shiga shirin ba.
PEN TIMES MAGAZINE
Comments(0)
Sign in to join the conversation
Sign In to CommentNo comments yet. Be the first to share your thoughts!

