ALHAJI ABUBAKAR ATIKU MAIDABINO(Hakimin 'Yantumaki:
ALHAJI ABUBAKAR ATIKU MAIDABINO(Hakimin 'Yantumaki na Farko)

ALHAJI ABUBAKAR ATIKU MAIDABINO(Hakimin 'Yantumaki: 1991–2008)
An haifi Alhaji Abubakar Atiku ranar 12 ga watan Oktoba, shekarar 1927, a garin Maidabino. Da ne ga Dan-Ali Muhammadu Murna (Magajin Maidabino: 1946–1973).Karatu da Farkon RayuwaAlhaji Atiku ya fara daukar karatun Addini daga kakansa, Dan-Ali Dabo Atiku, a shekarar 1936. Daga nan aka tura shi garin Dangeza domin ya ci gaba da karatun allo. Bayan shekaru biyu a Dangeza, sai aka mayar da shi garin Pawwa, inda ya yi karatu a karkashin Malam Abdulmuminu.
A shekarar 1938, ya shiga makarantar elamantare dake garin Dutsin-Ma mai suna Sada Primary School, tare da abokan karatunsa irin su Alh. Rabe Abdullahi, Dangaladiman Katsina (Hakimin Kafur), da Mai Garin Burdugau (Karamar Hukumar Kankara), Alh. Sidi Almu Dutsinma.
Harkar Aiki:
Alhaji Atiku ya yi kwasa-kwasai na koyon aikin magatakarda (Bukadi) a Katsina, inda ya kammala a shekarar 1945. Daga nan, hukumar Native Authority mai kula da lardin Katsina ta dauke shi aiki a matsayin magatakarda Inda ta tura shi Ruwan Kaya, daga nan sai Dan Aunai, da Shargalle a Karamar Hukumar Dutsi, duk a matsayin magatakarda. Daga bisani, N.A ta dawo da shi gida Maidabino domin ya yi aiki tare da kakansa, Alhaji Abubakar Dabo.
Bayan rasuwar kakansa, sai mahaifinsa ya karbi sarautar Dan-Ali Maidabino, inda Alhaji Atiku ya ci gaba da zama magatakarda har zuwa 1973, lokacin da mahaifinsa ya rasu. Yandakan Katsina, marigayi Alhaji Abdullahi Mai Kano, ya tura sunansa zuwa ga mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Sir Kabir Usman Nagoggo, domin nada shi a matsayin Dan-Ali Maidabino.
Hakimin 'Yantumaki:
A shekarar 1991, lokacin da aka kirkiro sabbin gundumomi na Hakimai. 'Yantumaki ta samu nasarar samun hakimi. Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Sir. Kabir Usman Nagoggo, ya nada Alhaji Abubakar Atiku a matsayin Jarman Katsina Hakimin 'Yantumaki na farko. Hakimcin sa ya fara da magaddai uku: Yantumaki, Maidabino, da Dan Ali.
Daga bisani, ya nemo karin magaddai guda bakwai, wadanda suka hada da: Dangeza, Dandire, Amarawa, Yardanko, Dandire, Unguwar Malamai, da Sabon Garin Tabarau. Hakan ya sa magaddai suka zama guda 10 a gundumar
'Yantumaki.
Gwamnati da Gudunmuwa:
Alhaji Atiku ya zama shugaba mai adalci wanda ya jawo al'ummarsa kusa da shi. A lokacinsa, ya taka rawar gani a bangarori daban-daban, kama daga zaman lafiya, ci gaban ilimi, da habbaka noma da kiwo. Ya kasance mutum mai tsananin kiyaye hakkokin talakawan sa, kuma bai lamunci zalunci ko musguna masu ba. A karkashinsa, an gina makarantun firamare, masallatai, da asibitoci a fadin Karamar Hukumar Danmusa.
Mukaman Da Ya Rike:
Ya taba rike matsayin Kansila a tsohuwar Karamar Hukumar Dutsin-Ma, inda ya kula da sashen ayyuka (Works Department).
Haka kuma, ya rike matsayin Shugaban kwamitin riko na Karamar Hukumar Danmusa lokacin da aka kirkiro ta a zamanin Shugaban Kasar Najeriya, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari.
Abubuwan Da aka san shi dasu;
Alh. Atiku Basarake ne, dan kasuwa ne, manomi ne,dan siyasa ne, kuma mai sha'awar sukuwar dawakai,wannan huddar tasa ya hadu da abokan arzki da aminai ako ina a fadin kasa Nigeria, da kasashen waje. Alhaji Atiku ya yi hulda da manyan mutane a ciki har da Sarkin Zazzau, Alhaji Dr. Shehu Idris; Sarkin Sudan na Kontagora; Baba Dantata Kano; da Sarkin Magarya, Alhaji Abba Kalli Wanban Katsina. Sauran abokansa sun hada da Alhaji Sani Babban Duhu da Sarkin Yaki na Kauran Namoda.
Ya rayu da matan aure 4 da ya'ya guda 57 . Allah ya jikan shi da Rahama Kuma ya kyautata bayan shi. Allah ya jikan dukkan magabatan mu kuma ya kyautata tamu in tazo.
Daga Jaridar Pen times magazine
An samu Tarihi daga Alh. Bishir Atiku Maidabino da
Salihu Ibrahim
Salihu Ibrahim is a Nigerian media professional, digital journalist, strategic communication practitioner, educationist and community development advocate from Yantumaki, Danmusa Local Government Area, Katsina State. He is the Chief Executive Officer (CEO) of Pen Times Media General Services and Chief editor of Pen Times Magazine, where he provides leadership, digital publishing, editorial coordination, publicity, advertising and strategic communication.
Comments(0)
Sign in to join the conversation
Sign In to CommentNo comments yet. Be the first to share your thoughts!
